Wakilin Muryar Amurka ya ji ta bakin wasu masu zanga zangar inda suka nuna farin cikinsu ga wannan hukunci da kuma fatan kowaye ya samu nasara zai tabbatar da ganin kasuwanci ya bunkasa a jihar.
A cewar sabon dan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP Eyitayo Jegede, basuyi mamakin hukuncin kotun ba kuma da yar dai Allah tun da yasa kansa wannan takara zai lashe zaben da za a gudanar.
Kasancewar mako daya tal ya rage ayi zaben gwamna a jihar, abin tambaya ana shine shin ko hukumar zabe zata bi dokar kotun wajen maye gurbin sunan Jimoh Ibrahim da Eyitayo Jegede?
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, farfesa Mahmud Yakubu, yace hukumar INEC hukuma ce mai bin dokar kasa, kuma lokacin da suka sami hukuncin kotun sun bi umarnin kotun nan take, haka kuma idan har an sake samun wata babbar kotu ta kara yanke hukuncin zasu bi hukuncin.
Shi dai Jimoh Ibrahim tsohon mai takarar zama gwamnan jihar Ondo yana bangaren Modu Sherrif, shi kuma Jegede na bangaren Ahmadu Makarfi.
Domin karin bayani.