Babban sifeton ya dora alhakin kashe jami'an a kan masu tsatsauran ra'ayin addini da 'yan fashi da makami da wasu 'yan tsagera.
Sanarwar da hedkwatar 'yansandan dake Abuja ta fitar tace wasu daga cikin aika aikan an tafkasu ne a jihohin Zamfara da Anambra da Rivers. Rundunar 'yansandan tace dole ne a daina hakan daga yanszu.
Kakakin rundunar matamakin kwamishanan 'yansanda Don Aruna yace babban sifetonsu bai ji dadin yadda ake kashe jami'ansa ba da afkawa ofisoshinsu da motocinsu da ma sauran gine-ginensu.
Yace duk inda aka samu tashin hankali 'yansanda ne ke fara zuwa wurin. Yace wani lokaci idan mutane nada damuwa tsakaninsu da zara sun ga dansanda sai su afka masa kamar shi ne umalubaisan matsalarsu. Yace babban aikinsu shi ne tabbatar da zaman lafiya da tsaro tare da kare dukiyoyin jama'a.
A cewar Ambassador Yusuf Mamman kashe dansanda babbar magana ce. Yace duk wanda ya taba dansanda ya taba hukumar Najeriya ne. Kamata yayi duk wanda ya kashe dansanda koina ya shiga an je an kamoshi.
Wani mai sharhi akan alamuran kullum Baba Yola Muhammad Tango yace 'yansandan Najeriya na bukatar samun horo irin na zamani. Yace rai rai ne kuma 'yansanda suna kashe mutane kullum amma babban sifeton bai taba fitowa yayi magana ba a kai.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.