An samu yin sulhu da 'yanbindigan ne tsakanin kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa a karkashin shugabancin mataimakin gwamnan jihar da kuma 'yanbindigan.
To saidai gwamnatin jihar kawo yanzu bata fito fili tayi wani cikakken bayani ba akan sulhun amma rahotanni sun nuna cewar 'yanbindigan sun bukaci a mayar masu da shanunsu da aka kwace kafin su sako mutanen. Bisa ga alamu gwamnati ta cika wannan sharadin na 'yanbindigan.
Yayinda yake gabatar da mutanen ga gwamnan jihar Zamfara mataimakin gwamnan yace ya koyi babban daratsi a jagorancin kwamitin 'yanto mutanen da yayi.
Mataimakin gwamnan ya kira shugabannin sassa, da shugabannin siyasa, da jami'an tsaro cewar idan ana son zaman lafiya da kwanciyar hankali to su nisanci zalunci. Yace abu na biyu da ya koya shi ne ta hanyar tattaunawa ana iya samun zaman lafiya tare da warware duk wata matsala.
Duk da cewa sai da nuna karfi ake shawo kan mazalunta cewa akwai hukuma amma karfi kawai baya kawo zaman lafiya sai an hadashi da lumana da jawo hankali.
Wannan sulhun da gwamnati tayi ya kara jaddada zargin da wasu keyi na cewa gwamnati nada masaniya akan inda 'yanbindigan suke. Wani yace gwamnati ta je wajen sojoji ta karbi shanun ta kaiwa 'yanbindigan kana ta amshi mutanen. Wai sun nuna kamar babu gwamnati. Yace babu wanda ya raka mataimakin gwamnan kuma tun karfe goma na safe da aka shirya bai je ba sai karfe takwas na dare.
A nashi bangaren gwamnan jihar yana zargin wasu da hannu cikin ruruta wutar rikici a jihar. Ya kira jami'an tsaro su tsaya suyi aikinsu yadda ya kamata.Injishi sarakuna su dinga sa ido kana alamuran tsaro saboda aiki ne na hadin gwuiwa.
Ga rahoton Murta Faruk Sanyinna da karin bayani.