Karkashi wani sabon tsari da hukumar ta fito da shi bana, akwai maniyyata dari daga wannan adadin da ta zabo daga kananan hukumomi ashirin da daya na jiha da zasu hada tasu aikin ibadar da karbar horo kan sabbin dabarun noman zamani don yaki da yunwa da talauci.
Wannan bayanin na kunshe cikin jawabin babban sakataren hukumar Bishop Jinga Mayo a bitar yini guda da aka shiyawa maniyyatan a majamiyar Katolika dake Yola fadar jihar Adamawa kan dokokin kasar Isra’ila, nau’in abinci, wuraren ibada da yadda zasu tafiyar da ayukansu duk tsawon zamansu.
Jagoran maniyyata na jihar Adamawa kuma kakakin majalisar dokoki Onarebul Sunday Peter ya kalubalancesu su zame manzanai nagari da yiwa kasar Najeriya adu’ar neman zaman lafiya. Inda yake jan kunnen masu niyar anfani da damar da suka samu na yin layar zana, yana cewa duk wanda ya bar kasarsa zuwa wata kasar zai zama bawa.
Wasu matakan da hukumar ta dauka don masu niyar shiga layar zanar inji Bishop Jinga Mayo ita ce ta hada mutane biyu daki guda domin su rika sa ido kan take-taken ‘yan uwansu, don haka ne ma duk wanda ya sake abokin zamansa ya bata za a tuhume shi da aikata makarkashiya.
Daya daga cikin maniyatan da ya yi hira da Muryar Amurka Solomon Kumamgar ya ce sun gamsu da tsarin da hukumar kula da Kiristoci masu zuwa ibada kasar Isra’ila bana ta yi.
Ana saran hukumar kula da Kiristoci masu zuwa aikin ibada kasar Isra’ila ta kasa zata kaddamar da tashin maniyyatan bana da mutane dari uku da biyar a filin saukar jiragen sama na kasa-da-kasa dake Yola fadar jihar Adamawa Alhamis din nan.
Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.