Larabawa a kasashe daban-daban da suka kama daga Iraqi zuwa Tunisia suna bibiyar zaben shugaban kasa a nan Amurka kuma akasarin larabawan duk suna son ganin yar takatar Democrat Hillary Clinton ta lashe zaben, saboda suna kyautata zaton itace kawai zata anfani kasashen nasu, a cewar wani bincike.
Wannan binciken da Cibiyar Nazarin Harakokin Kasashen Larabawa ta nan Washington DC ta gudanar a kasashe takwas, ya gano kashi 66 cikin 100 sun fi ra’ayin Clinton ta dare kan shugabancin Amurka, a yayind da kashi 11 cikin dari kadai ne ke ra’ayin dan takarar Republican Donald Trump.
Binciken ya jiyo ra’ayoyin mutane 3,200 a kasashen Algeria, Egypt, Kuwait, Morocco, yankunan Falasdinu, Saudi Arabia da kuma Tunsia daga ran 21 zuwa 31 ga watan Oktoba. Duka-duka an jiyo ra;ayoyin mutane dari hur-hudu ne a kowace kasa daga cikin kasashen da aka gudanarda binciken a cikinsu.