Masu gabatar da kara na kasar Belgium sunce za a iya tasa keyar madugun harin ta’addancin da aka kai birnin Paris zuwa kasar Faransa.
Ministan harkokin sharia na kasar Faransa, Jean-Jacques Urvoas ya fada jiya Alhamis cewa, yana kyautata zaton za a tasa keyar Salah Abdeslam zuwa birnin Paris cikin kwanaki goma masu zuwa.
Yace “Abdelsam yana so a sani cewa, zai ba hukumomin kasar Faransa hadin kai. Abinda yake so a sani ke nan”.
Wani lauyan nasa kuma ya bayyana bayan kamashi ranar goma sha takwas ga watan Maris cewa, zai kalubalanci tasa keyarsa zuwa Faransa. Babu tabbacin abinda ya a ya sake tunanensu.
Ana zargin Abdeslam da taimakawa wajen kulla makarkashiyar hare haren ta’addancin da aka kai ranar goma sha uku ga watan Nuwamba a birnin Paris da ya kashe mutane dari da talin a wurare dabam dabam. An ce ya daukarwa ‘yan kunar bakin waken hayar dakuna, ya kuma sai masu nakiyoyi.
Wani mai gabatar da kara na kasar Faransa yace Abdeslam ya yi shirin tarwatsa kansa a bakin filin wasan kwallo, amma daga baya ya janye.