Jaridun Belgium da dama sun bada labarin cewa, an tsinci na’urar kwamfutar ta hannu ne a lokacin da ‘yan sanda suka kai samame a unguwar Rue Max Roos da ke Schaerkbeek sa’o’i da dama bayan kai harin na tashar jiragen sama data kasa a Brussels da ya hallaka mutane 32 ya jikkatawasu da dama.
Wani jami’in gwamnati da ya nemi a sakaya sunansa saboda har yanzu ana binciken lamarin, ya tabbatar da labaran da suka bayyana, ya kuma kara da cewa, har yanzu ba wata alama da ta nuna cewa Firayim Ministan na fuskantar barazanar mahara.
Yace, kwamfutar an sameta cike da bayanai daban daban da aka samu ta hanyar laluben yanar gizo game da ofishin Firayim Ministan da yake da matsuguni a Rue De la Loi da ake yin taron ‘yan majalisarsa a wajen, wanda tuni yake cikin wuraren da aka kafa tsauraran matakan tsaron da aka karfafa tun bayan harin da aka kai birnin Paris.