Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama ya kammala ziyararsa zuwa Cuba


Shugaba Barack Obama a Cuba yayinda yake jawabi ta kafar talibijan jiya a Havana babban birnin Cuba
Shugaba Barack Obama a Cuba yayinda yake jawabi ta kafar talibijan jiya a Havana babban birnin Cuba

Shugaba Barack Obama ya kai ziyara mai dimbin tarihi zuwa kasar Cuba abun da bai taba faruwa cikin shekaru fiye da tamanin da suka gabata.

Yayinda yake kammala ziyarsa shugaba Obama yace lokaci ya yi da ya kamata Amurka da Cuba su kawo karshen zamanbera da kyanwa da suke yi su fara wata sabuwar danganta su yi tafiya tare.

Lokaci ya yi da zasu dauki matakan da zasu anfani kasashen biyu maimakon suna kushewa juna tamkar makiya.

Shugaba Barack Obama ya yi furucin ne lokacin da yake yiwa 'yan kasar Cuba jawabi ta kafar talibijan a birnin Havana da aka nuna aduk fadin kasar.

Manufar zuwansa Cuba inji shi ita ce kulla abokantaka da da kasar da kuma al'ummarta. Ya kira 'yan kasar da su mance da abubuwan da suka faru can baya su fuskanci gaba da manufofin alheri ga junansu.

Shugaban ya amince warware duk takaddamar dake tsakanin kasashen biyuba zai yiwu ba cikin dan karamin lokaci. Za'a dauki lokaci kafin a cimma burin amma a soma

XS
SM
MD
LG