Kotun kolin Najeriya ta ayyana zaben kananan hukumomin da hukumar zaben jihar Ribas ta gudanar a ranar 5 ga watan Oktoban 2024 a matsayin wanda bai tabbata ba.
A hukuncin da Mai Shari’a Jamilu Tukur ya zartar, kotun ta ayyana zaben a matsayin wanda bai tabbata ba saboda mummunan saba dokar zabe da aka yi.
Da yake karanta hukuncin, Mai Shari’a Tukur yace ya ayyana matakin da hukumar zaben jihar Ribas ta dauka a matsayin wanda ba halastacce ba saboda rashin yin biyayya ga dokar zabe da sauran ka’idoji kasancewar ta ci gaba da yin rijistar masu kada kuri’a har bayan an sanar da ranar zabe.
Kotun ta kara da cewa an gaza bin tsare-tsaren gudanar da zaben kananan hukumomin inda karara hakan ya sabawa sashe na 150 na dokar zaben.
A wani hukuncin da ta yanke yau Juma’a, kotun kolin ta hana babban bankin Najeriya (CBN) da babban akanta na tarayya da sauran hukumomin gwamnati sakin kudade ga gwamnatin jihar Ribas.
Dandalin Mu Tattauna