Mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden, yace kisan gillar da akayi a garin Orlando dake Florida, “Abune a wajen karara babu wata sarkakiya a ciki” a yayin da masu bincike ke neman dalilin da yasa aka kai harin da ya halaka mutane 49 da raunata wasu 53.
Biden bai bayar da wani cikakken bayani ba a jiya Talata, amma yace nan bada dadewa ba shugaban kasa zai bayar da ‘karin haske kan lamarin. A gobe Alhamis ne idan Allah ya kaimu aka shirya shugaba Obama zai ziyarci Orlando.
A cikin jawabin da shugaba Obama yayi bayan taron inganta matakan tsaro tare da duba abinda ya faru a birnin na Orlando, Obama yace Mateen ya samu wannan mummunar akida ce ta anfani da hanyar sadarwan yanar gizo ko internet.
Shugaba Obama yace jami'an tsaron Amurka na nan na iya bakin kokarin su domin ganin sun dakile aukuwar irin wannan al’amari, Sai Obama ya bayyana irin wahalar dake tattare da gano ire-iren wadannan mutanen kafin su kai ga aikata wannan ta'asar.
Sai dai tun farko Babban jamiin tsaron cikin gida Chief Jeh Johnson ya kira da a samar da dokar mallakar bindiga barkatai, sakamakon ganin abinda ya faru a Orlando.
Yace yanzu haka dai mahukunta na nan na cigaba da tattara bayanai game da rayuwar shi Mateen.