Yayinda jam'yyu da 'yan takara ke shirin zaben kananan hukumomin jihar Adamawa a cikin wannan watan sai gashi gwamnan jihar Sanata Muhammad Bindo Jibrilla yana neman a dage zaben.
Ita hukumar zaben jihar tace ashirye take ta gudanar da zaben wannan watan kamar yadda aka shirya.
Gwamna Bindo yace zabe a watan azumi bai dace ba. A matsayinsa na musulmi yana ganin bai dace a ce ana fafutikar neman zabe ba a watan Ramadan. Yace watan ibada ne kuma bai kamata a je ana damun mutane ba da batun neman kuri'a. Yace shi ya fadi ra'ayinsa ne.
Wannan furucin na gwamnan jihar ya jawo cecekuce har a jam'iyyarsa ta APC. Sardaunan Jimeta Alhaji Muhammad Haladu ya zargi gwamnan da neman dage zaben saboda wai idan an yi mutanen Buhari ne zasu samu rinjaye. Ma'ana, bangaren gwamnan ba zasu kai labari ba. Yace yana haka ne don Baba Buhari ba maigidan gwamnan ba ne. Yana da nashi maigidan daban. Amma su a wurinsu Baba Buhari ba ma maigida ba ne kawai, uban Najeriya ne gaba daya.
Su ma hadakar jam'iyyun adawa sun ce su basu gamsu ba saboda gwamnatin jihar tayi shishshigi a alamarin zabe. Sun ce gwamnan bashi da hakkin ya fito ya fadawa mutanen Adamawa cewa a dage zabe. Furucin nasa ya sa suna tambaya ko hukumar zaben jihar nada 'yanci.
Jam'iyyar APC mai mulkin jihar tace ba da yawunta gwamnan yake magana ba kamar yadda sakataren tsare-tsarenta Ahmed Lawal ya bayyanawa manema labarai. Yace hukumar zabe ta basu rana cewa 25 ga wannan watan za'a yi zaben kuma hukumar bata ce ta daga zaben ba. Jam'iyyu suna nan kan ranar da aka basu.
Shugaban hukumar zaben jihar Alhaji Isa Shettima yace su ba 'yan amshin shatan gwamnatin jihar ba ne. Yace da yaddar Allah za'a yi zabe kamar yadda suka fada. Yace kayan aiki suke jira.
Ga karin bayani.