Kasar Isira'ila ta soke takardar izinin tafiyar Falasdinawa 83,000 a yayin watan azumin Ramadan, bayan da wasu Falasdinawa biyu 'yan bindiga su ka bude wuta kan masu sayayya da masu cin abinci a wata kasuwar da ke daura da Ma'aikatar Tsaron Isira'ila da ke Tel Aviv da daren jiya Laraba, da ya yi sanadin mutuwar mutane 4 da kuma raunata biyar.
"Duk wani izinin da aka bayar don Ramadan, musamman izinin tafiyar iyalai daga Judea da Samaria zuwa cikin Isira'ila an soke," a cewar COGAT, sashin da ke kula da harkokin farar hula a Yamma da Kogon Jordan, a wata takardar bayani a yau dinnan Alhamis.
Wannan umurnin ya kuma shafi daruruwan Falasdinawa a Gaza da kuma 'yan'uwan 'yan'uwan daya daga cikin wadan ake zargi da kai hari, wadandan aka haramta wa dukkansu kai ziyara ga 'yan'uwansu, da kuma halartar addu'o'in lokacin watan Ramadan a Birnin Kudus, da kuma tafiya kasar waje ta filin jirgin saman kasa da kasa da ke Tel Aviv.
Sojojin Isira'ila sun kuma ce za su girke karin daruruwan sojoji, ciki har da na musamma, a Yammacin Kogin Jordan a matsayin martanin wannan harin.