Kasar Sudan ta maida wani mutum da ake zargi da yin fasakwabrin bakin haure zuwa kasar Italiyya, a cewar ‘yan sanda kasar ta Italiyya yau Laraba.
An kama Medhainie Yehdego Mered dan shekaru 35, dan kasar kasar Eretria, a Khartoum a karshen watan da ya shige. Dama yana cikin mutanen da ake nema ruwa jallo kusan shekara daya kenan don fasakaulin mutane daga kasashe.
An dauki Mered a matsayin mai fasakwabrin mafi karfi a yankin kudancin saharar Libiya, a cewar wata sanarwar ‘yan sandan.
Ba a Afrika kadai yayi harkokinsa ba har wayau yana da mutanen da ya ajiye suna dakon jiragen ruwan dake isowa dauke da bakin haure, inda yake taimaka musu cigaba da tafiyarsu zuwa kasashen Turai.
‘Yan sandan sun kuma ce bayanan wayarsa da aka nada a boye su suka nuna cewa Mered na alaka da wasu masu fasakaulin a arewacin kasashen Turai.
Dakarun Sudan da na Italiyya da na Burtaniyya ne suka hada hanu wajen gano Mered.