A yau Laraba, gwamnatin kasar koriya ta Kudu taki ta fito fili ta tabbatar da bayanan da aka samu na cewa Koriya ta Arewa na sarrafa ma'adinin Plutonium amma dai ta ce ta na sa ido sosai akan abubuwan da ke wakana.
Dama can an san Koriya ta Arewa ta sha kokarin yin ayyukan neman karin Plutonium, a ta bakin ministan hadin kan kasa Jeong Joon-hee a lokacin da yake wa manema labarai bayani. “Akwai hadin kan kud-da-kud tsakanin Koriya ta kudu da Amurka akan wannan batun, a cewarshi.
Jami'an diplomasiyar Amurka da na Majalisar dinkin duniya sun ce Koriya ta arewa ta sake komawa aiyukkan sarrafa mai don neman ma'adinin na plutonium a masana'antarta dake Yongbyon.