'Yan Majalisar Dokokin Jamus sun kada kuri'a yau Alhamis, ta amicewa da kisan Armeniyawan da Turkiyya ta Daular Usmaniyya ta yi, yayin yakin duniya na 1 a matsayin kisan kare dange.
Tunda farko Shugaban Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya yi gargadin cewa muddun aka amince da kudurin a matsayin doka, dangantakar kasashen Turkiyya da Jamus ta fuskar diflomasiyya da tattalin arziki da cinakayya da siyasa da soji za ta yi tsami.
Armaniya ta ce an kashe mutane miliyan 1 da rabi tsakanin 1915 da 1917. Turkiyya ta amsa cewa an kashe dubban Armeniyawa, to amma ta ki yadda cewa wannan kisan wani yinkuri ne na karar da wani jinsi.