An kashe mutane 3 a wasu hare-hare guda biyu da aka kai kan sansanonin Majalisar dinkin duniya, a Mali tun jiya Talata.
An kashe wani jami’in wanzar da zaman lafiya ta harbin roka a yammacin jiya Talata, akallah wasu mutane 10 kuma sun jikkata a sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya, da ake kira MINUSMA a garin Gao.
Hari na biyu kuma ya faru ne a safiyar yau Laraba a wata unguwa dabam a sansanin UNMAS a garin na Gao wanda yayi sanadiyyar hallaka mutane 3, kasar China ta ce daya daga cikin wadanda suka mutu din sojan wanzar da zaman lafiyar Kasarta ne.
Ranar Lahadin da ta gabata kuma, an kashe sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya, su 5 a Mali wani kuma ya jikkata a wani kwanton baunan da aka yi masu duk a ranar. Wani hari makamancin wannan ma ranar Jumma’ar da ta gabata ya kashe dakarun Mali su 5 wasu su 4 kuma suka jikkata yayinda motarsu ta bi ta kan wata nakiya bayan haka wasu yan bindiga suka bude masu wuta a arewacin kasar.
Bayan harin na yau Laraba, adadin dakarun wanzar da zaman lafiya da aka kashe a Mali, ya hau zuwa akalla 66, abinda ya sa ya zama aikin kiyaye sulhun Majalisar dinki duniya, da aka fi yawan asaran rayukkan sojanta a cikinsa a duniya.