Jami’an hukumar sufurin jiragen sama na kasar Masar sun fada yau Laraba cewa wani jirgin ruwan kasar Faransa ya kamo sautin da ta yiwu daga akwatin na’urar akwatin bayanan nan da ake kira "Black Box" ne na jirgin EgyptAir da ya fada Bahar Rum cikin watan da ya gabata.
Faduwar jirgin da ta auku ranar 19 ga watan Mayu, ya hallaka dukkan mutane 66 dake cikinsa. Hukumomin na kokarin gano akwatunan bayanan ne da za su taimaka masu gano musabbabin faduwar jirgin wanda ya fadi yana dab da kamalla tafiyarsa daga Paris zuwa Alkahira.
Masu bincike sun ce an ga hayaki yana fitowa daga dakin matukan jirgin ‘yan mintoci kafin faduwar jirgin, amma babu abinda ya nuna musabbabin hayakin.
Jami’an kasar ta Masar sun fada yau Laraba cewa nan da mako daya wani jirgin ruwan bincike zai isa wajen da hadarin auku don dauko akwatinan na’urori in har aka gano su.