A yau Laraba Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris ta kira Donald Trump domin taya shi murnar cin zaben shugaban kasa na bana, a cewar daya daga cikin hadimanta, bayan zazzafar takarar da suka yi.
Shugabannin duniya sun taya Donald Trump murnar lashe zabe bayan da hasashen kafafen yada labarai ya nuna cewar ya samu kyakkyawan rinjaye a zaben shugaban Amurka na bana.
Wannan nasara ta Trump ta biyo bayan gagarumin zabe wanda ya kawo tsauri sosai tsakanin jam’iyyun siyasa da kuma yankunan Amurka.
Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris na da wakilai 179 na zabe, yayin da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya samu wakilai 214.
A yammacin ranar Talata ne sakamakon zabe ya fara fitowa fili a zaben shugaban kasa tsakanin mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris da tsohon shugaban kasar Donald Trump.
Amurkawa sun kada kuri’unsu domin zaben wanda suke so su aika zuwa fadar White House na tsawon shekaru hudu masu zuwa. Haka kuma za su zabi wadanda za su cike kujerun Majalisar Dattawa 34, sai kuma ‘yan Majaisar Wakilai 435 da kuma gwamnonin jihohi 13.
Domin Kari