Yanzu haka an fara rufe rumfunan zabe a wasu jihohi yayin da suran ake ci gaba da kada kuri’un.
Sakamakon farko sun nuna cewa Trump ya lashe zaben jihahohin Indiana da Kentucky, yayin da kuma Harris ta lashe za ben jihar Vermont.
Sakamakon bai zo da babban abin mamaki ba.
Dan takarar na Republican ya lashe jihar Indiana a bakwai daga cikin zabukan shugaban kasa takwas da suka gabata, da kuma Kentucky a zabukan shida cikin takwas da aka gudanar.
A halin da ake ciki, jihar Vermont, ‘yan takarar Democrat ne a kowane zabuka takwas da suka gabata suke samun nasara.
Jihar Indiana tana da yawan wakilai 11 na zabe, kuma Kentucky tana da yawan wakilan zabe 8. Hakan na nufin a halin yanzu Trump yana da wakilai 19. Harris, tana da wakilan zabe uku daga nasarar da ta samu a Vermont.
Akalla ‘yan Takara na bukatar samun wakilan zabe 270 ake bukata domin lashe zaben shugaban kasa.
Dandalin Mu Tattauna