Domin kada kuri'a a zaben shugaban Amurka, wajibi ne wanda zai kada kuri'ar ya kasance dan asalin Amurka, kuma shekarunsa na haihuwa sun cika 18 a ranar zaben ko kafin lokacin kuma ya cika sharuddan zaman wuri, wadanda ke bambanta daga jiha zuwa wata jihar.
Haka kuma wajibi ne masu niyar kada kuri'a suyi rijista a bisa dacewa da wa'adin rijistar zaben jihohi. Wasu jihohinma suna takaita kada kuri'a ga fursunonin da aka yankewa hukunci akan manyan laifuffuka ko mutanen dake larurar tabin hankali.
Gaba daya, Amurkawan dake zaune a wajen kasar na iya zabe ta hanyar kuri'ar nesa, sai dai a zaben shugaban kasa, Amurkawan dake zaune a yankunan da Amurka ke iko dasu, ciki har da Puerto Rico, Tsibirin Virgin, Tsibirin Arewacin Marianas da kuma Samoa ba za su iya yin zabe ba.
Dandalin Mu Tattauna