Kafin ya shiga siyasa, Obi dan kasuwa ne wanda ya rike mukamai da dama a wasu masana’antu masu zaman kansu, ciki har da Next International Nigeria Ltd, da Guardian Express Bank Plc, da sauransu.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi tir da kakkausar murya a kan kisan gillar da aka yi wa Cif Oyibo Chukwu, dan takarar sanata na jam’iyyar Labour a mazabar Enugu ta Gabas da kuma hadiminsa.
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta INEC ta ce tana aiki kafada da kafada da kanfanonin sadarwa kamar su MTN, Glo, Airtel da 9Mobile domin magance duk wata matsalar hanyar sadarwar internet da ka iya tasowa yayin kada kuri’a.
An haifi Atiku a 1946 a yankin Jada na jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, ya kuma nemi takarar shugabancin Najeriya sau biyar in an hada da zaben nan na 2023 inda ya ci nasarar samun tikiti sau uku.
Hukumar zaben Najeriya ta bayyana kamala shirye shiryen babban zabe na kasa da za a fara gobe da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarraya, zaben da tuni daruruwan masu sa ido daga kasashe da kungiyoyi dabam dabam na duniya suka isa kasar domin ganin yadda zai gudana.
Hukumar zaben Najeriya ta INEC ta ce bayanai na nuna cewa akwai kwanciyar hankalin gudanar da babban zaben a kasar yau Asabar.
Ana sa ran shugaba Buhari zai kada kuri’arsa a rumfar zabe da ke kusa da gidansa a garin Daura tare da mai dakinsa Aisha Buhari da sauran ahalinsa.
Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya ya gargadi jami’an sa su guji shiga cikin harkokin ‘yan siyasa, maimakon haka su mayar da kai wajen gudanar da ayyukan su na kiyaye doka da oda domin a gudanar da zaben kasar cikin lumana.
Shugaban Amurka Joe Bide ya ce ya yaba wa yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi a Najeriya, da ta samu sanya hannun jami’iyyun siyasa da ‘yan takara da zasu fafata a zaben shugaban kasar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Yayin da 'yan Najeriya ke shirin gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar taryya a ranar Asabar, gwamnatin tarayyar ta bada umarnin rufe dukkan iyakokin kasa na kasar.
Blinken ya kara da cewa, “Amurka na matukar burin ganin an gudanar da wannan zabe cikin lumana.
Hukumar kula da kafafen labarai na ketare ta Amurka wato USAGM, ta hori wakilan kafafen labaru na Najeriya kan yadda za su tsare dokokin aikin jarida idan sun tashi ba da labarai kan yadda za a gudanar da babban zabe har zuwa bayan sanar da sakamako.
Domin Kari