Sanya hannu a kan wannan alkawari da jami’iyyun siyasa da ‘yan takara suka yi na nufin zasu amince da sakamakon zaben kamar yanda hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC zata sanar kana su taimaka wa shirin mika mulki cikin lumana.
Ya ce zabuka sune kashin bayan dimokaradiya, kana ‘yan Najeriya sun cancanci wannan dama ta yin zabi ga makomar su ta hanyar gaskiya da adalci. Yayin da Amurka bata goyon bayan wani dan takara ko wata jami’iyya, muna ba da dukkan goyon baya ga tsarin zaman lafiya da adalci da zai yi daidai da muradin ‘yan Najeriya.
"A ranar zaben, ina ba da kwarin gwiwa ga duk al'ummar Najeriya da su fita su yi zabe ba tare da la’akari da addini ko yanki ko kuma kabila ba, ciki har da matasa wadanda zasu dunguma zuwa runfunan zabe a karon farko da zasu kada kuri’a.
Amurka na tare da al'ummar Nijeriya, yayin da suke tsara bin hanyar samun ingantacciyar dimokaradiyya, mai albarka, da amintacciyar makoma. "Ina godiya da jajircewar shugaba Buhari cewa za a mutunta muradin al’ummar kasar", in ji shi
Ya kuma kara da cewa a cikin kwanaki masu zuwa, ina karfafa wa masu kada kuri'a da su kasance cikin kwanciyar hankali da hakuri yayin da ake kidayar kuri'u, "Ina kuma kira ga jam'iyyun siyasa da 'yan takara su cika alkawuran da suka dauka", in Biden
Ga Hassan Maina Kaina da sakon cikin sauti: