Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Daura jihar Katsina inda zai kada kuri’arsa a zaben shugaban kasa na 2023.
A ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya.
Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar dauke da sa hannu kakakinsa Malam Garba Shehu, ta nuna cewa gwamnan jihar Aminu Bello Masari da shugaban hukumar tattar bayanan sirri ta NIA, Ahmed Rufai ne suka tarbi Buhari.
“Buhari zai kada kuri’arsa a rumfar zabe da ke kusa da gidansa a garin Daura tare da mai dakinsa Aisha Buhari da sauran ahalinsa.
“Da misalin karfe 5:25 na yamma jirgin Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka a Daura, a wani mataki na shirye-shiryen zaben wanda zai yi a matsayin mai kada kuri’a kamar yadda ya yi a shekarar 2003.” Sanarwar ta kara da cewa.