Wannan shi ne karo na biyar da Ronaldo yake zuwa gasar cin kofin duniya, ta kuma yi wu, shi ne karo na karshe.
Rukunin na G a gasar cin kofin duniya ta Qatar, ya kunshi Brazil, Serbia, Kamaru da kuma Switzerland, saboda haka samun makin uku na farko na da matukar muhimmanci a wannan wasa na ranar Alhamis.
Wales dai ta samu bugun fenariti ne, bayan da Walker Zimmerman ya kwade Bale ta baya, kuma alkalin wasa Abdulrahman Al-Jassim na kasar Qatar mai masaukin baki, bai yi wata-wata ba ya nuna bugun daga kai sai mai tsaron gida.
A ranar Lahadi aka bude gasar ta cin kofin duniya a Qatar, inda mai masaukin bakin ta sha kaye a hannun ‘yan wasan Ecuador da ci 2-0 a wasan farko da aka buga a gasar.
A ranar Lahadi 20 ga watan Nuwamba ne za’a soma gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya ta bana a Qatar, karon farko da aka fadada gasar zuwa kasashe 32, haka kuma karon farko a tarihi da za’a gudanar da gasar a yankin kasashen larabawa.
An raba kasashen da za su fafata din ne zuwa rukunoni 4, inda Senegal ta ke cikin rukunin A, Tunisia a rukunin D. Morocco na rukunin F, Kamaru a rukunin G, sai Ghana take rukunin H. Qatar mai masaukin baki ce za ta buga wasan farko da Ecuador a filin wasa na Al Bayt
A ranar Lahadi mai zuwa ne za a fara gasar cin kofin duniya ta maza a kasar Qatar, inda magoya baya a Afirka ke sha’awar kallon kungiyoyi biyar na nahiyar da za su fafata a gasar.
Ga dukkan alamu kasar Qatar ta shirya tsaf don karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya.
Za a fara gasar da wasan Qatar da Ecuador a filin wasa na Al Bayt da mai cin 'yan kallo dubu 60.
Wannan kira na zuwa ne makonni uku gabanin Iran ta kara a wasanta na farko da Ingila a rukunin B.
Domin Kari