A ranar Lahadi mai zuwa ne za a fara gasar cin kofin duniya ta maza a kasar Qatar, inda magoya baya a Afirka ke sha’awar kallon kungiyoyi biyar na nahiyar da za su fafata a gasar.
Ga dukkan alamu kasar Qatar ta shirya tsaf don karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya.
Za a fara gasar da wasan Qatar da Ecuador a filin wasa na Al Bayt da mai cin 'yan kallo dubu 60.
Wannan kira na zuwa ne makonni uku gabanin Iran ta kara a wasanta na farko da Ingila a rukunin B.
Tuni dai kamfanonin jiragen sama, wuraren shakatawa, gidajen sayar da abinci da kantunan kayan alatu suka fara wasa wukakensu don tarbar baki.