A ranar Lahadi 20 ga watan Nuwamba ne za’a soma gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya ta bana a Qatar, karon farko da aka fadada gasar zuwa kasashe 32, haka kuma karon farko a tarihi da za’a gudanar da gasar a yankin kasashen larabawa.
An raba kasashen da za su fafata din ne zuwa rukunoni 4, inda Senegal ta ke cikin rukunin A, Tunisia a rukunin D. Morocco na rukunin F, Kamaru a rukunin G, sai Ghana take rukunin H. Qatar mai masaukin baki ce za ta buga wasan farko da Ecuador a filin wasa na Al Bayt
A ranar Lahadi mai zuwa ne za a fara gasar cin kofin duniya ta maza a kasar Qatar, inda magoya baya a Afirka ke sha’awar kallon kungiyoyi biyar na nahiyar da za su fafata a gasar.
Ga dukkan alamu kasar Qatar ta shirya tsaf don karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya.
Za a fara gasar da wasan Qatar da Ecuador a filin wasa na Al Bayt da mai cin 'yan kallo dubu 60.
Wannan kira na zuwa ne makonni uku gabanin Iran ta kara a wasanta na farko da Ingila a rukunin B.
Tuni dai kamfanonin jiragen sama, wuraren shakatawa, gidajen sayar da abinci da kantunan kayan alatu suka fara wasa wukakensu don tarbar baki.