Kenya ta samu gagarumar ci gaba a yunkurin rage masu yawan kamuwa da cutar HIV cikin shekaru goman da suka gabata. An samu raguwar sabbin masu kamuwa da cuta da kaso 78% sannan an samu raguwar mutanen da AIDS yake sanadin mutuwar su da kaso 57%.
Farfesa Ibrahim Ummate, jami’in cibiyar jinyar koda ta asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri a Najeriya, ya yi karin bayani a game da matsalar cutar koda da kuma kalubalen maganinta.
A Zambia, hukumomi sun ce ana samun karuwar matasa mata masu kamuwa da sankarar mama a kasar. Haka kuma, ana samun karuwar wadanda ake gano cutar a tare da su bayan ta kai mataki mafi muni a kurarren lokaci.
Hukumar lafiya ta duniya ta kiyasta kiyasta cewa mutane miliyan 850 ne suke fama da cutar koda a fadin duniya, sannan cutar ta na sanadiyyar mutuwar sama da mutum miliyan 2 da dubu dari shida a kowace shekara.
Wannan na zuwa ne wattani 2 bayan da gwamnatin kasar ta janye matakin gaggawar lafiyar al’umma wanda aka ayyana tun shekarar 2022.
Wani kwararen likita a Najeriya, Dr Ibrahim ya yi karin haske a game da fida da mutum-mutumi.
Domin Kari