Kwararru sun ce kama daga gano cutar zuwa maganin ta, kirkirarriyar fasahar AI tana dada taka mahimmiyar rawa wajen taimakawa likitoci su dada fahimtar yadda za su yi maganin cututtukan zuciya, wadanda suka kasance mafiya girma dake kashe mutane a fadin duniya.
Kasar Brazil ta kaddamar da gangamin rigakakin cutar zazabin dengue a daidai lokacin da kasar ta ke samun hauhawar kamuwa da cutar. A bisa bayanan ma’aikatar lafiyar kasar, Brazil ta samu hauhawar cutar da kusan ninki 5 cikin makonni 5 cikin wannan shekarar, wanda ya zarta na shekarar da ta gabata.
Dr. Amina Jaafar, babbar jami’a a sashen kula da cututtukan zuciya a cibiyar kula da lafiya ta kasa da ke Abuja a Najeriya, ta yi bayani akan cututtukan zuciya da tasirin su a nahiyar Afirka.
Domin Kari