Wani rahoton bincike da aka gudanar a bana ya zargi wakilin katafaren kamfanin taba sigari na Switziland da Amurka, a Burkina Faso, Philip Morris da samar da kudi ga masu aikata ta’addanci, ta hanyar yin fasakwaurin tabar.
A birnin Jos a Najeriya wata kungiya mai zaman kanta ta dukufa wajen wayar da kan mutane don kaucewa furta kalaman kiyayya dake haddasa munanan rikice-rikice a tsakanin al’umma.
Kungiyar ‘yan kasuwa a Najeriya ta yi gargadin cewa karuwar tashe-tashen hankali da garkuwa da mutane su na korar ‘yan kasuwa masu sha’awar zuba jari, abin da kuma ya ke yiwa tattalin arzikin kasar babbar illa.
Ga wasu daga cikin wasannin da aka yi a wannan makon na gasar wasannin kwallon kwando ta Afrika dake gudana a birnin Kigali na Rwanda.
A jamhuriyar Nijar wata matashiya da ta shahara a harkar tsere tana da kwayoyin halitta da suka yi kama da na maza, abinda ke neman kawo mata tarnaki a fafatawar da za ta yi a wasannin Olympic na bana a Tokyo.
Satin da ya gabata Amurka ta samu matsalar mai a wasu sassan kasar, wadda take da nasaba da ayyukan masu yin kuste a kwamfuta, inda suka tsayar da ayyukan daya daga cikin manyan kamfanonin dake raba mai a kasar, Colonial Pipeline.
A karshen makon jiya ne aka fara gasar wasannin kwallon kwando ta Afrika a birnin Kigali na Rwanda. An yi wasanni da dama kawo yanzu. Ga wasu daga cikin wasannin da aka yi a wannan makon.
Amurka ta fitar da rahoton shekara-shekara akan ‘yancin yin addini – kuma Nijeriya da Iran da Saudiyya da China su na daga cikin kasashen da rahoton ya ce suka fi takurawa jama’a.
A jihar Kano a Najeriya, bayan kusan shekaru biyu ba a yi ba, a bana an gudanar da Hawan Nasarawa, wata al’ada da sarkin Kano ya ke kai ziyarar wurare a wani bangare na bikin sallah.
Kasar Mali na daya daga cikin kasashen Afrika dake noman auduga sosai. Amma yawancin audugar akan kai ta ketare ne.
Gwamnatin jihar Borno a Arewacin Najeriya ta na yunkurin sake bude makarantu a wuraren da rikicin Boko Haram ya tilasta rufe makarantu na tsawon shekaru.
Labarin wasu mata a jihar Sokoto a Najeriya wadanda suka rungumi sana’ar gyaran mota, wacce aka san maza ne da ita a wannan yanki na kasar. Wasu daga cikin matan dai sun kammala karatunsu, kuma sun ce su na alfahari da sana’ar.
Domin Kari