A Senegal, jagoran ‘yan adawa Ousmane Sonko, ya bukaci masu zanga-zanga da su ci gaba da nuna adawa da shugaban kasar, bayan da hukumomi suka sako shi.
Wani matashi a birnin Jos da ke Najeriya, ya kera wata na’urar wanke hannu yayin da ake yaki da COVID-19 a duniya.
A jamhuriyar Nijar, an soma ayyukan kamun kifi a tafkunan kasar, inda hukumomi kan je domin kaddamar da hakan bayan tsawon lokaci da dakatar da ayyukan saboda coronavirus, da kuma bayar da dama don kifaye su kara yawa.
Shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno, Hajiya Yabawa Kolo ta ce gwamnatin jihar ta na iya bakin kokarinta wajen kyautata rayuwar ‘yan gudun hijirar rikicin Boko Haram.
A makon da ya gabata ne wasu mahara suka halaka mutane goma sha biyu a garin Amarawa dake karamar hukumar Illela ta jihar Sokoto. Mutanen dai sun rasa rayukansu ne a kokarin ceto wani mutun guda da maharan suka yi garkuwa da shi.
Bayan shekara daya da barkewar annobar coronavirus a duniya, mun yi waiwaye don ganin yadda annobar ta shafi Afrika.
Shekara uku kenan da 'yan Boko haram suka sace dalibai mata 110 a wata makaranta dake Dapchi, a Najeriya. Har yanzu yarinya daya, Leah Sharibu na hannun mayakan. Iyayenta na fatan za ta kubuta amma sun ce ba abin da gwamnati ke yi don tabbatar da an sako ta.
‘Yan kasuwar kwamfuta da litattafai da ta yi gobara a makon jiya a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a Najeriya, sun yi kira ga gwamnati da ta kai masu dauki domin farfado da sana’o’in su.
Hukumar NASA da Amurka sun kai wata tawagar kasashe duniyar wata ranar alhamis da ta gabata, yayin da na’urar dake binciken abubuwa ta sauka lafiya bayan barin jiragen zuwa duniyar wata na hadaddiyar daular larabawa da China da suka je duniyar.
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta na aiki tukuru da dakarun kasar Kamaru, kuma ba da dadewa ba za ta fara aiki da na Chadi domin kawo karshen rikicin Boko Haram.
Amurkawa musulmi sun yi na’am da dokar da shugaba Biden ya sanya wa hannu ta dage haramtawa kasashen da galibinsu na musulmi ne da yawa zuwa Amurka.
Tsohuwar ministar kudi ta Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin sabuwar shugabar kungiyar cinikayya ta duniya-WTO, biyo bayan goyon baya da ta samu daga gwamnatin shugaba Biden na Amurka.
Domin Kari