Cikin wata sanarwa, ma’aikatar tsaron Nijar ta ce ‘yan ta’adda fiye da 100 sun yi amfani da bama-bamai da makaman roka wajen kai hari kan sojoji wadanda suke gudanar da aikin kakkabe ‘yan ta’adda a kusa da iyakar kasar da Mali, suka kuma halaka sojoin Nijar 29
Ra'ayoyin mutane akan karin Naira dubu 35 a wata ga ma’aikatan gwamnatin Najeriya, za su amfana? Ko wannan kari zai rage radadin cire tallafin man fetur? To wadanda ba za su amfana da wannan karin albashin kuma fa?
Yadda a karon farko a tarihin Amurka, an tsige kakakin majalisar wakilan kasar, Kevin McCarthy na jam’iyyar Republican, wanda shi ne ke mataki na biyu na wadanda za su iya maye gurbin shugaban kasa idan aka samu gibi.
A wata hira da Muryar Amurka Kwamared Audu Titus Amba, mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta NLC ya ce karin albashi zai shafi sauran ma’aikatan gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi da ma bangarori masu zaman kansu.
Wasu dalilan da suka sa a farkon makon nan kungiyoyin ‘yan kwadago a Najeriya suka janye shirinsu na shiga yajin aikin gama-gari wanda suka so farawa daga ranar 3 ga watan Oktoba
A wata hira da Muryar Amurka, Sanata Ireti Kingibe, ‘yar Majalisar Dattijan Najeriya ta ce saboda irin kalubalen da ita ta fuskanta a siyasa babban abin da ta fi mayar da hankali akai yanzu, shine samar da dama ga mata da yawa na yin nasara a siyasa
Kungiyoyin kwadago a Najeriya suna barazanar tafiya yajin aiki, inda suka bukaci gwamnati da ta dawo da biyan kudin tallafin man fetur da ta kawo karshe a watan Mayu.
Yayin da kamfanoni da sauran masu sana’o’i ke ci gaba da tafka asara sakamakon karancin wutar lantarki a Nijar, wasu kugiyoyin fararen hula a kasar sun yi barazanar maka Najeriya a gaban kotun ECOWAS kan zargin saba yarjejeniyar kasuwancin wutar lantarki tsakanin kasashen biyu,
Mun tattauna da Malam Kabir Adamu wani mai sharhi kan sha’anin tsaro, akan matsalar yawan sace dalibai a Najeriya, da wasu ke ganin akwai sakacin hukuma sosai.
Matsalar yawan sace dalibai a Najeriya da ‘yan bindiga ke yi a makarantu - A ranar Juma’a 22 ga watan Satumba wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wasu dakunan kwanan daliban jami’ar gwamnatin tarayya dake Gusau a jihar Zamfara, inda suka sace kimanin dalibai 24 akasarinsu mata
Mun ji ta bakin Bode Gbadebo, wani 'dan jarida kuma mai sharhi a Najeriya, akan wani bangare na jawabin shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a taron UNGA
Bayani kan yadda shugabannin kasashen duniya suka gabatar da jawabai da suka tabo batutuwa daban-daban a wurin babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 da ya gudana a birnin New York na Amurka
Domin Kari