Labarin sace kodojin mutanen ya jefa mutane da dama da aka taba yi musu aiki a asibitin cikin rudani, yayin da wasun su ke zuwa ana duba su ko suma an sace musu na su kodojin.
Mohammad Qaddam Sadiq Isa, wani mai bincike da sharhi a kan harkokin Gabas ta Tsakiya wanda yake zaune a Dubai ya mana karin haske akan rikicin da ke tsakanin Isra’ila da Falasdinawa, mai dadadden tarihi da ya ki ci ya ki cinyewa
A wasu manyan biranen duniya kamar babban birnin New York a Amurka mutane suna mayar da martani ne ga rikicin Isra'ila ta hanyar yin zanga-zangar nuna goyon baya ga bangarorin biyu.
Yadda a birnin Kirkand na jihar Washington a Amurka, masu zanga-zangar goyon bayan Isra’ila da na Falasdinawa, suka so su ba hammata iska, yayin da suka fita kan tituna dauke da tutocin bangarorin da suka marawa baya.
Yadda mutane a Jamhuriyar Nijar ke ci gaba da mayar da martani ga abubuwan dake faruwa tsakanin Isra’ilar da Falasdinawa.
Mun duba rikicin dake faruwa a gabas ta tsakiya tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas ta Falasdinawa sakamakon wani harin bazata da mayakan Hamas suka kai kan Isra’ila ranar Asabar 7 ga watan Oktoba.
Cikin wata sanarwa, ma’aikatar tsaron Nijar ta ce ‘yan ta’adda fiye da 100 sun yi amfani da bama-bamai da makaman roka wajen kai hari kan sojoji wadanda suke gudanar da aikin kakkabe ‘yan ta’adda a kusa da iyakar kasar da Mali, suka kuma halaka sojoin Nijar 29
Ra'ayoyin mutane akan karin Naira dubu 35 a wata ga ma’aikatan gwamnatin Najeriya, za su amfana? Ko wannan kari zai rage radadin cire tallafin man fetur? To wadanda ba za su amfana da wannan karin albashin kuma fa?
Yadda a karon farko a tarihin Amurka, an tsige kakakin majalisar wakilan kasar, Kevin McCarthy na jam’iyyar Republican, wanda shi ne ke mataki na biyu na wadanda za su iya maye gurbin shugaban kasa idan aka samu gibi.
A wata hira da Muryar Amurka Kwamared Audu Titus Amba, mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta NLC ya ce karin albashi zai shafi sauran ma’aikatan gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi da ma bangarori masu zaman kansu.
Wasu dalilan da suka sa a farkon makon nan kungiyoyin ‘yan kwadago a Najeriya suka janye shirinsu na shiga yajin aikin gama-gari wanda suka so farawa daga ranar 3 ga watan Oktoba
Domin Kari