A watan Maris kotun kolin Najeriya ta ce a ci gaba da amfani da tsoffin kudaden naira har zuwa karshen 2023.
Matan kan gudanar da wannan aiki ne ko a wane irin hali na yanayi da ake ciki, kamar na rana ko ruwa ko sanyi.
A lokacin da ake gab da gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a Najeriya, karancin man fetur na ci gaba da ci wa ‘yan kasar tuwo a kwarya, da hakan zai iya zama matsala wajen yin tafiye-tafiye zuwa jihohi don gudanar da zaben.
Sai dai duk da umurnin da babban bankin ya bayar, rahotanni sun ce har yanzu akwai wasu ‘yan Najeriyar da ke dari-darin karbar kudaden.
A makon jiya ma gobara ta lalata dukiyar ‘yan kasuwa ta biliyoyin Naira a kasuwar Monday Market ta birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya.
A ranar Litinin jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara suka shigar da kara a kotun inda suka kalubalanci sabon wa’adin, wanda zai kare a ranar Juma’a mai zuwa.
Bankunan sun dauki wannan mataki ne don ba jama’a damar sauya tsoffin kudadensu yayin da wa’adin kammala amfani da su yake karatowa.
‘Yan Najeriya sun yi barazanar yin bore muddin gwamnatin kasar ta gaza daukar matakin dakatar da babban bankin kasar CBN kan wa’adin da ya bayar na daina karba da kuma amfani da tsoffin takardar kudin da aka canja.
Domin Kari
No media source currently available