Washington, DC. —
Shirin na yau ya kai ziyara Kasuwar Kure a jihar Neja da ke Najeriya inda ake saida kayayyaki dabam-daban.
‘Yan kasuwar sun bayyana yadda tashin farashin kayayyaki ke shafar sana’arsu, inda suka ce kusan a duk mako farashin kayayyaki ke canzawa galibi saboda karin farashin kudin waje da ake canzawa a kasar.
‘Yan kasuwar sun kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba koken talakawa don su samu sauki.
Saurari cikakken shirin da Babangida Jibrin ya gabatar: