"Idan kun taba amfani da wadannan magunguna, kuma sun haifar muku da wata matsala, ku yi maza ku garzaya asibiti." In ji NAFDAC.
A karkashin jagorancin shugaban Ghana Nana Akufo-Addo, da babban sakataren harkokin cinikayya tsakanin kasashen Afirka (AfCFTA) Wamkele Mene za a yi taron kan ci gaban Afirka karo na farko a Ghana. Taron da masu ruwa da tsaki suka ce Ghana da Afirka baki daya, za su amfana da shi.
Tsarin ya fara aiki ne a ranar Litinin 9 ga watan Janairu, kuma rahotanni sun yi nuni da cewa bankuna sun fara bin umarnin
A baya, fadar shugaban kasar ta tsara kasafin kudin na bana akan naira tiriliyan 20.51.
Rahoton ya kara da cewa, kilo daya na shinkafar gida ya karu da kashi 18.95, abin da ke nufin farashin ya karu daga naira 421 a watan Nuwamban bara zuwa naira 500.80 a watan Nuwambar 2022.
Taron na mayar da hankali ne kan yadda za a hada kai don bunkasa harkokin cinikayya da saka hannun jari da zai ciyar da tattalin arzikin Afirka gaba don a dama da nahiyar a fagen kasuwancin duniya.
A cewar Nnori, jiragen kasan yanzu za su tashi minti 30 kafin lokacin tashinsu da aka tsara a baya.
Bankin CBN ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kwantar da hankulansu a game da tsarin saboda an yi ne don ci gaban kasa, ba wai don kuntatawa al’umma ba.
Yayin da wasu ke yaba wannan sabon tsari na cire kudade a bankunan kasar, wasu kuwa akasin hakan suke nunawa.
Hukumar kwastam ta ce a fili ta ke gudanar da gwanjan kaya kuma kowa zai iya shiga yanar gizo ya ga yanda a ke gudanar da cinikin.
Gidajen gyara hali a Najeriya, na ci gaba da kasancewa matattarar masu aikata laifuka mabambanta inda wasu masu laifi kan iya koyon wasu laifuka na daban musamman wadanda ba su da aikin yi kafin a kai su kurkuku.
Domin Kari
No media source currently available