Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da ‘Yan Najeriya Ke Cewa Kan Sabon Tsarin CBN Na Takaita Kudin Da Za Iya Cirewa A Banki


Sabbin kudin Naira
Sabbin kudin Naira

Yayin da wasu ke yaba wannan sabon tsari na cire kudade a bankunan kasar, wasu kuwa akasin hakan suke nunawa.

‘Yan Najeriya da dama na bayyana ra’ayoyi mabanbanta, bayan da Babban Bankin kasar na CBN ya fitar da wani sabon tsari da zai fara takaita adadin tsabar kudin da za a iya cirewa a banki.

A ranar Talata CBN cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktan da ke kula da bankunan kasar, Haruna Mustafa, ya ce Naira dubu 100 kawai mutum guda zai iya cirewa a mako.

CBN ya kara da cewa kamfanoni ko kungiyoyi za su iya cire dubu 500 a kowane mako sannan dubu 20 kawai mutum zai iya cirewa ta kafar POS a rana.

Wannan mataki a cewar bankin kolin kasar, ci gaba ne a jerin tsare-tsaren sauya fasalin takardun naira da aka kaddamar a kwanan nan.

Sai dai yayin da wasu ke yaba wannan sabon tsari na cire kudade a sassan kasar, wasu kuwa akasin hakan suke nunawa.

“Sai su koma kasan katifa kawai, ka ga babu wanda ya isa ya saka maka doka.” Bello Abdullahi ya ce a tsokacin da ya yi a Facebook.

“Ga me tunani, wannan tsari ba talaka zai sha wuya ba, barayin gwamnati su za su sha wuya da ‘yan siyasa.” Abdullahi Suleman ya ce.

Shi kuwa, Aliyu Maccido cewa ya yi “gaskiya wannan canji ya yi kyau.”

“Ni dai ban ji dadi ba, saboda alamu na nuni da cewa za a kara shiga matsin rayuwa.” Tasi’u Ibrahim ya ce.

A ranar 9 ga watan Janairun 2023, sabon tsarin zai fara aiki a cewar CBN.

XS
SM
MD
LG