Gabanin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, masu neman takara a jam’iyyar na ci gaba da mara baya ko fadar abin da su ke son a yi don gudun korafi ko ma tafiya kotu a sakamakon zaben.
Mai magana da yawun hukumar zabe ta Najeriya, INEC Alhaji Aliyu Bello, ya ce sun shirya tsaf domin gudanar da zaben Gwamna a Jihar Osun.
Yanzu haka dai cakwakiyar zaben fidda gwani na jam’iyar APC dake mulki a Najeriya na daukan wani sabon salo a jihar Adamawa ,inda yan majalisar wakilan jihar ke cewa zasu bar jam’iyar muddin aka rushe shugabanin jam’iyar karkashin Ibrahim Bilal.
Tsohon sakataren gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal ya jagoranci sauran masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC na Jihar Adamawa inda suka shigar da takardar koke ga jam’iyyar APC ta kasa.
Shugaba Buhari ya daga hannun sakataren jam’iyyar APC Mai Mala Buni, biyo bayan zabar sa da gwamna Ibrahim Gaidam ya yi don takarar gwamnan jihar Yobe, a jam’iyyar APC a zaben 2019.
Kakakin majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogara ya bi sahun shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki wajen yin kaura zuwa babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Yayin da 'yan siyasa a tarayyar Najeriya ke ci gaba da neman lasisin tsayawa takarar shugabanci, jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta haramtawa wasu mata uku tsayawa takara.
Hukumar zabe mai zaman kanta a jahar Pilato ta ayyana nanar goma ga watan gobe, wato Oktoba, don gudanar da zabe kananan hukumomi a jahar.
Yayin da ake haramar zaben tsayar da yan takara a jam’iyun siyasar Najeriya, wata matsalar dake barazana ga zaben dake tafen itace ta yan bangan siyasa,da ke neman gagaran kundila a jihar Adamawa.
Cibiyar bunkasa harkokin demokaradiyya ta National Democratic Institute na Muradin aiki tare da masu ruwa da tsaki musamman kafofin yada labaru domin aiwatar da shirin ta na fafutikar baiwa mata damar shiga a dama da su cikin harkokin siyasa a Nigeria
Ya zuwa yanzu dai ‘ya yan jam’iyyar APC mai mulki a Najeriye, na ci gaba bayyana ra’ayin su game da amincewar da jami'iyyar ta yi na zaben 'yar tinke a zaben shugaban kasa.
Yanzu haka dai ana cece-ku-ce a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, reshen jihar Adamawa, bayan da kanin matar shugaban ‘kasa Dakta Mahmood Halilu Ahmad ya fito takarar kujerar gwamnan jihar.