Alhaji Aliyu Bello, ya ce kawo yanzu hukumar na da kayayyakin da ake bukata domin gudanar da zaben, kuma za a gudanar da zaben lami lafiya cikin kwanciyar hankali. Ya kuma kara da cewa an tura ma’aikatan zabe zuwa kanannan hukumonin jihar, inda a yanzu haka ma’aikatan suke jira a fara zaben.
Alhaji Aliyu, ya bayyanawa wakilin Muryar Amurka cewa 'yan takara 48 ne zasu faffata a zaben gwamna gobe asabar, ya ce hukumar zabe zata yi wa kowannen su adalci tare da bin ka’idojjin da hukumar zabe ta tanada don gudanar da zaben.
Ya kara da cewa hukumar zabe bata da dan takara a cikin waddanda suka tsaya takara, don haka dukkan su na mataki daya na masu neman gwamna. Ya ce Kuri’a ce kadai ka iya kai dan takara matakin cin nasara wajen lashe kuri’un da al’umma suka jefa masa, kana hukumar zabe zata yi amfani da kuri’un da aka jefa don kirga zaben tare da gano wanda ya samu nasara.
Facebook Forum