Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ta haramtawa wasu mata su uku shiga takarar kujerar majalisar dokoki ta tarayya da kuma majalisar dokoki ta jihar, to amma cibiyar National Democratic Institute mai rajin bunkasa harkokin demokaradiyya ta ce matakin tsagaro ne tsarin demokaradiyyar najeriya.
Hajiya Asabe Bala Kanoma wacce ta fito neman kujerar majalisar dokoki ta jihar Zamfara, mai wakilatar mazabar Maru ta daya da Malama Shafa’atu Salihu Labbo dake neman wakiltar mazabar Kaura ta arewa a majalisar dokokin ta jihar Zamfara, kana kuma da Hajiya Amina Iliyasu dake neman takarar kujerar tarayya ta Talatan Mafara/Anka a majalisar wakilai.
Sai dai za a iya cewa hakan dai wani koma baya ne ga yunkurin da cibiyar National Democratic Institute wato NDI keyi na ganin karuwar adadin mata masu rike mukaman sisaya a arewa da wasu sassan kudancin kasar.
Facebook Forum