Tun gabanin matakin sakataren ya ce matakai biyu ke tsarin mulkin jam’iyyar na zaben fidda gwani da su ka hada da amfani wakilai ko zaben ‘yar tinke.
‘Yan siyasar Yobe na sharhi kan wannan mataki da yadda ya shafi tunanin yiwuwar zarcewar jam’iyyar, wacce ba ta taba zama karkashin mulkin PDP ba.
Muhammad Auwal Lalla, ya ba da shawara ga ‘yan siyasar da ba su gamsu da matakin ba, su sauya sheka zuwa sauran jam’iyyu tun da akwai fiye da jam’iyyun adawa 90 da ke da rejista.
Wadanda su ka kwana biyu su na manna hotunan neman takara a jihar sun hada da Sidi Karsuwa, da tsohon daraktan Baitulmalin Abuja Ibrahim Bomai.
Gabanin cankar Mai Mala Buni, wanda bai manna hoto ba, wani matashi mai mara baya ga wani daya daga ‘yan takarar ya baiyana ra’ayin mika takarar ga dan Majalisar Wakilai Sidi Yakubu Karasuwa, da ya ce ba ya kyamar talakawa.
A Arewacin Najeriya yankin Arewa maso Gabas mai jihohi shida, shine ma mafi karfin jam’iyyar PDP don ita ke rike da jihohin Gombe da Taraba a zaben baya, ba kamar yadda Gwamna Otom na Benue da Abdulfatah na Kwara a Arewa ta tsakiya su ka koma PDP ba.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum