Wani katin gayyata da jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram, ya nuna cewa a ranar Juma’a 4 ga watan Nuwamba za a daura auren a Kano da ke arewacin Najeriya.
Taylor Swift ta kafa tarihi a matsayin mawakiyar farko da ta taba samun wakokinta goma suka shiga jerin manyan wakokin 100 da aka fi so a cikin mako guda da faifan ta mai suna "Midnights."
A shekarar 2018, D’ Banj, ya rasa dansa Daniel mai shekara daya ta irin wannan hanya, inda shi ma ya fada tafkin ninkaya da ke gidan mawakin ya kuma rasa ransa.
An karrama 'ƴan wasan kwaikwayo da yawa a bikin karrama fitattun 'yan wasan fina-finai na Afirka (AMAA) na 2022 da ya gudana a Legas ranar Lahadi.
“A lokacin da aka zabe ni a matsayin wadanda za su kara a neman wannan lambar yabo, na fadawa kaina cewa zan yi alfahari da kaina ko a nan aka tsaya. Ashe ba san cewa ni ce ma zan lashe lambar yabon ba.” In ji Rahama.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yaba da gudummowar da mawakan kasar ke bada wa, inda ya ce sun kara martaba fannin nishadin Najeriya a idon duniya.
An yi sallar jana’izarsa a unguwar Hotoro da misalin karfe 9 na safe a birnin Kano.
A ranar 30 ga watan Mayun 2022 Gwanja ya saki sautin wakar ta “Warr” ya kuma fitar da bidiyonta a ranar 1 ga watan Agusta.
An yi bikin karrama mawakan ne a karo na 15, wannan kuma shi ne karon farko da aka yi a Amurka.
A Nijr, an gudanar da bikin kaddamar da ayarin zaman lafiya inda cibiyar fina-finai ta CINE NOMADE da tallafin ofishin jakadancin Amurka a Nijar za ta zagaya jihohin kasar da nufin tattaunawa da jama’a akan batun zaman lafiya musamman matasa.
Mawaki Ice Prince ya shiga hannun jami'an tsaro da sanyin safiyar yau Jumma'a a jihar Legas akan yin tuki da lambar mota mara lasisi, da kuma yi wa jami'in dan sanda barazana.
An fara zaben masu taya alkali ne yau litinin a shari'ar da gwamnatin tarayya ke wa R. Kelly a garinsa na Chicago, inda shahararran mawakin na R&B ke fuskantar tuhuma kan zarginsa da yin danne gaskiya a shari'ar da aka masa kan aikata lalata a jihar a shekara ta 2008.
Domin Kari
No media source currently available
Ya Fitattun Mutane Ke Amfani Da Kafofin Sadarwa?