Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rukayya Dawayya Za Ta Auri Afakalla


Jaruma Rukayya Dawayya, dama da Afakalla, hagu (Hoto: Farin Wata Photography)
Jaruma Rukayya Dawayya, dama da Afakalla, hagu (Hoto: Farin Wata Photography)

Wani katin gayyata da jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram, ya nuna cewa a ranar Juma’a 4 ga watan Nuwamba za a daura auren a Kano da ke arewacin Najeriya.

Jarumar masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Rukayya Umar Santa wacce aka fi sani da Dawayya za ta auri shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Malam Isma’il Na-Abba Afakalla.

Wani katin gayyata da jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram, ya nuna cewa a ranar Juma’a 4 ga watan Nuwamba za a daura auren a Kano da ke arewacin Najeriya.

"Alhamdulilah muna gayyatar 'yan uwa da abokan arziki. idan ba'a samu dama ba, ay i mana addu'a" Dawayya ta rubuta a kasan katin gayyatar.

An dade ana ta rade-radin auren jarumar da shugaban hukumar tace fina-finan, amma sai a wannan karo labarin ya tabbata.

Ko da yake, a baya, akwai rahotanni da dama da suka bayyana cewa masoyan biyu na shirye-shiryen aure, duk da cewa ba su fito fili sun bayyana hakan ba.

Tuni masoya da abokansu suka fito suna ta taya su murnar wannan sabon mataki da za su taka na rayuwar aure.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG