Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taylor Swift Ta Kafa Tarihi A Bikin Bada Lambar Yabo Na Grammy


Taylor Swift
Taylor Swift

Taylor Swift ta kafa tarihi a matsayin mawakiyar farko da ta taba samun wakokinta goma suka shiga jerin manyan wakokin 100 da aka fi so a cikin mako guda da faifan ta mai suna "Midnights."

Mawakiyar da ta lashe lambar yabo ta Grammy, ta sami wannan nasarar tare da wakokinta daga sabon jerin wakokinta mai suna "Midnights."

Swift ta doke tsohon mawaki Drake wanda ya ci waƙoƙi tara cikin 10 da wakarsa "Certified Lover Boy" wanda ya fito a bara.

Taylor Swift
Taylor Swift

Wakar da ta sami lambar yabo ta farko ita ce "Anti-Hero" wanda kuma shine farkon bidiyo na kida daga jerin wakokinta kuma wakar farko da aka rika rairawa a rediyo.

Wakar "Anti-Hero" ta yi fice da kusa miliyan 59.7. Mai biye a kusa shine "Lavender Haze."

Sauran wakoki a cikin 10 sun hada da "Maroon," "Snow on the Beach," "Midnight Rain," "Bejeweled," "Question…?," You’re on Your Own, Kid,” “Karma” da " Vigilante Shit."

XS
SM
MD
LG