Dukkan shugabannin suna fara jawaban su ne da batun annobar coronavirus da ta hana gudanar da taron na gaba da gaba a bara da kuma yanda annobar ta kawo nakasu ga shirin muradun karni da ma tattalin arzikin duniya.
Taron na wannan shekara ya banbanta da yadda aka saba gani a shekarun baya, inda dubban mutane ke halartar wannan taro dake tattaro shugabannin kasashe da firai ministoci da manyan tawagogi da kuma wakilai na kungiyoyi masu zaman kansu zuwa nan birnin New York.
Taliban ta mulki Afghanistan daga 1996 zuwa 2001 inda ta gudanar da mulkinta karkashin shari’ar Musulunci a kasar. Ga wasu daga cikin muhimman abubuwa da suka shafi akida da tarihin kungiyar.
“Ci gaba da zaman dakarun Amurka a kasar na tsawon shekara daya ko shekara biyar ba zai sauya komai ba idan har sojojin Afghanistan ba za su iya rike kasarsu ba,” Biden ya fada a ranar Asabar cikin wata sanarawa.
Gwamna Andrew Cuomo ya sanar da cewa zai ajiye aiki cikin makonni biyu masu zuwa biyo bayan zargin shi da ake yi da cin zarafin mata.
Wasu ‘yan kasar Colombia da ‘yan sandan kasar Haiti suka tsare dangane da kisan gillar shugaban kasar Jovenel Moise sun halarci shirye-shirye na horo da karatu na sojojin Amurka, kamar yadda kakakin ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ya tabbatar a cikin wata sanarwa da aka aikawa VOA.
An sami kamfanin Donald Trump da kuma babban jami’i mai kula da harkokin kudinsa da laifukan da suka samo asali daga masu bincike na New York kan harkokin kasuwancin tsohon shugaban kasar.
Idan ya nuna halayya mai kyau yayin zaman gidan yarin, akwai yiwuwar a saki Chauvin nan da shekara 15 - amma zai ci gaba da rayuwa karkashin sa idon hukuma.
A kowacce shekara a watan azumin Ramadan, yawancin masallatai a Amurka su na raba abinci ga jama'a a lokacin buda baki. A wannan karon, an raba abincin ne daga cikin mota.
Hukumar kula da ingancin magunguna ta Amurka ta ba da izini ga kamfanin Pfizer da BioNTech na amfani da allurar rigakafin COVID-19 ga yara ƙanana daga shekaru 12 zuwa 15.
An yankewa tsohon jami’in ‘yan sanda farar fata, Derek Chauvin, hukunci akan kisan Ba’amurke bakar fata George Floyd, a yayin da yake kokarin kama shi a birnin Minneapolis.
Iyalan mawakin salon wakar gambara ko kuma rap, DMX, sun ce mawakin ya rasu.
Domin Kari