Ofishin Jakadancin Amurka Ya jinjinawa dan Najeriya Kelechi Ndukwe da ya kafa tarihi ranar na zama bakar fata na farko da ya jagoranci jirgin ruwan yakin Amurka.
Tun bayan farmakin da aka kai a ginin majalisar dokokin Amurka ranar 6 ga watan Janairu aka tsaurara matakan tsaro a ginin majalisar da kewaye.
Mama Sarah, ta yi hidimar ganin an inganta ilimin ‘ya’ya mata da marayu a ƙauyenta na Kogelo da ke Kenya.
Gwamnatin Amurka ta yi Allah wadai da harin da aka kai a Nijar, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 137.
A yau Asabar shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar da jawabi a kan shirinsa na dala triliyan daya da biliyan 900 na tallafin COVID-19 da majalisar wakilai ta tabbatar da shi da safiyar yau.
Ana cigaba da samun bayanan yadda rayuwa take a duniyar sama.
Amurka na gab da samun mace-mace rabin miliyan sakamakon cutar COVID-19, da karin mace-mace da ke da alaka da coronavirus fiye da kowacce kasa, a cewar cibiyar samar da bayanan coronavirus ta Jami’ar Johns Hopkins.
Amurka ta sake komawa cikin yarjejeniyar Paris a hukumance bayan da gwamnatin Trump ta fice daga yarjejeniyar ta sauyin yanayi, tana mai cewa shirin ya yi matukar tsada ba zata yi aiki da shi ba.
Shugaban Amurka Joe Biden ya yi alkawarin ba da tallafin dala biliyan hudu domin a kara kaimi wajen samar da allurar rigakafin cutar COVID-19 ga kasashe marasa galihu.
Wani hadarin tarihi na lokacin sanyi da ya kara tsananin sanyi a akalla rabin fadin Amurka, ya sa sama da mutum miliyan biyu da rabi a Texas sun rasa wutar lantarki.
Majalisar Dattawan Amurka, ta wanke Donald Trump a yunkurin tsige shi da aka yi a karo na biyu cikin shekara guda, inda ‘yan Republican suka hana a dora masa laifi mummunan harin da magoya bayansa suka kai a ginin majalisar dokokin kasar.
Majalisar dattawan Amurka ta kada kuri’ar bada sammacin gayyato shaidu su bada bahasi a wannan shari’ar tsige tsohon shugaban kasa Donald Trump.
Domin Kari