Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Tabbatar Da Laifin Kisan George Floyd Akan Derek Chauvin


Tsohon Jami'in 'yansandan Minneapolis, Derek Chauvin
Tsohon Jami'in 'yansandan Minneapolis, Derek Chauvin

Kotu ta tabbatar da tuhuma 3 da ake yi wa Chauvin na kisan kai, inda yake fuskantar hukuncin dauri gidan yari na tsawon shekaru 40 akan laifin kisa mataki na 2, da daurin shekara 25 na kisan kai mataki na 3, da kuma wasu shekaru 10 na kisan ganganci.

Alkalan kotun sun tattauna na tsawon sa’o’I 11, kafin su tabbatar da dukkan tuhuma 3 da ake yi wa Chauvin mai shekaru 45, lamarin da ya zama wani zakaran gwajin dafi na takawa ‘yan sanda birki akan wuce gona da iri a yayin gudanar da ayukan su a Amurka.

Mutane da dama ne suka tattaru a harabar kotun ta Minneapolis da aka zagayen ta da jami’an tsaro, inda kuma suka yi murna da hukuncin da kotun ta yanke, a yayin da wasu da dama suka yi ta zubar da kwalla bayan da aka bayyana hukunci akan shari’ar da aka kwashe tsawon makwanni 3 ana yi.

Mutanen da suka tattaru a harabar kotu a lokacin shari'ar Chauvin
Mutanen da suka tattaru a harabar kotu a lokacin shari'ar Chauvin

Chauvin wanda aka bayar da shi beli, an buga masa ankwa jim kadan bayan da alkalin gundumar Hennepin, Peter Cahil ya karanta hukuncin, wanda dukkan alkalai 5 na kotun suka amince da shi, kana aka fice da shi daga kotun yana sanye da takunkumin rufe hanci, ba tare da bayyana wata damuwa a fuskarsa ba.

George Floyd ya mutu ne a ranar 25 ga watan Mayun shekarar da ta gabata ta 2020, bayan da Chauvin ya danne masa wuya da gwiwar kafarsa.

Marigayi George Floyd
Marigayi George Floyd

An yi ta yayata hoton bidiyon da Chauvin ya ke durkushe a wuyan Floyd da ke kwance rub-da-ciki har na tsawon mintuna 9, alhali yana daure da ankwa, kuma yana karajin cewa baya iya numfashi.

Derek Chauvin ya danne wuyan George Floyd
Derek Chauvin ya danne wuyan George Floyd

Hakan ko ya faru ne sakamakon kokarin kama shi da ake yi, bisa zargin bayar da takardar kudin jabu ta dala 20.

Mutuwar ta Floyd dai ta janyo zanga-zanga a duk fadin Amurka da sauran sassan duniya, ta kin jinin cin zarafin jama’a da ‘yan sanda suke yi.

XS
SM
MD
LG