An yankewa tsohon dan sandan nan Derek Chauvin hukuncin daurin shekara 22 da rabi a gidan yari bayan da aka same shi da laifin kisan George Floyd – Ba’amuken nan dan asalin Afirka.
Alkali Peter Cahill ya fada a zaman kotun Minneapolis da ke jihar Minnesota a ranar Juma’a cewa, hukuncin wanda ya haura wanda ake yanke wa masu laifukan farko, ya kai haka ne saboda, Derek Chauvin ya yi amfani da mukaminsa ya aikata ba daidai ba da kuma irin yadda ya nuna rashin tausayi.
Masu shigar da kara sun nemi a yanke masa daurin shekara 30, yayin da lauyoyinsa suka ce a yanke masa hukuncin jeka-gyara-halinka da kuma iya lokacin da ya kwashe a tsare a lokacin da ake shari’ar.
Karin bayani akan: Derek Chauvin, George Floyd, Minneapolis, da jihar Minnesota.
Idan ya nuna halayya mai kyau yayin zaman gidan yarin, akwai yiwuwar a saki Derek Chauvin nan da shekara 15 - amma zai ci gaba da rayuwa karkashin sa idon hukuma.
A ranar 20 ga watan Afrilu aka samu Derek Chauvin da laifin kisa a mataki na biyu, da mataki na uku da kuma yin kisa ba-da-gangan-ba a mataki na biyu.