Hayakin da ke fitowa daga gobarar daji a kasar Canada ya kwarara har zuwa Gabashi da Yammacin tsakiyar Amurka a ranar Laraba, ya mamaye manyan biranen kasashen biyu a cikin wani yanayi mai muni.
Wata kungiyar kasar Amurka da ake kira Health and Development International ta sanar cewa jamhuriyar Nijer ta samu nasarori a yunkurin magance matsalar yawan matan da ke mutuwa sanadiyyar zubar da jini a yayin nakuda.
A yau Talata ne aka rantsar da sabon Magajin Garin birnin Colorado Springs na jihar Colorado ta nan Amurka.
Mobolade yayi takara ne a matsayin mai zaman kan sa, ya kuma sami nasarar kayar da wani dan jam'iyyar Republican da ya dade yana rike da mukamin bayan zagaye na biyu na zaben.
A wani bangare na bada gudummuwa wajen ganin Ghana ta shawo kan matsalar abinci, kasar Isra'la ta shirya wani taro tsakanin manoman shinkafa a Ghana da na kasarta a birnin Accra, inda suka tattauna kan matakai da dama.
Sannan za ku ji cewa masu sha’awar tsayawa Republican takarar shugaban kasa na karuwa – za ku ji mutane na baya-baya da ke shirin ayyana burinsu na neman tikitin jam’iyyar.
Yayin da Ghana ta kammala mataki na biyu na bunkasa samar da makamashin nukiliya, gwamnatin Amurka da Japan sun kara jaddada alkawarin tallafa wa shirin makamashin nukiliyar Ghana, da ke da nufin ba da ingantaccen makamashi mai tsabta.
Bayan kimanin watanni ana bincike, an yi nasarar kama wani da ake zargi da harbin da ya kashe Eunice Dwumfour mai shekaru 30 da haihuwa.
Turner ta rasu ranar Talata, bayan doguwar jinya a gidanta dake Küsnacht kusa da Zurich, a cewar manajanta. Ta zama 'yar kasar Switzerland ne shekaru goma da suka wuce.
Yemi Mobolade, dan Najeriya ne kuma dan kasuwa wanda bashi da kwarewa a harkar siyasa, ya zama bakar fata na farko da aka taba zaba a matsayin Magajin Garin Colorado Springs bayan da yayi nasara akan Wayne Williams da daren Talata a zagayen zaben da aka yi a birnin.
Tawagar jami'an da aka kai wa hari ranar Talata a garin Ogbaru na jihar Anambra ta kunshi ‘yan Najeriya guda tara, ciki har da ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka a Najeriya biyar da kuma jami’an ‘yan sandan Najeriya hudu.
Amurka ta sha alwashin hana wasu 'yan Najeriya damar shiga kasarta, sakamakon rawar da suka taka wajen yi wa dimokaradiyya zagon kasa a babban zaben kasar na 2023 da aka gudanar.
Domin Kari