Sakatariyar Baitul Malin Amurka, Janet Yellen, ta yi gargadin cewa idan har ba a fadada damar karbar bashin ba, nan da farkon watan Yuni gwamnati za ta rasa kudaden da za ta kashe.
Kotu ta umurci Tsohon shugaban Amurka Donald ya biya matar da aka tabbatar ya yi ci zarafinta ta hanyar neman yin lalata da ita shekaru da dama da suka wuce, lamarin da Trump ya sha musantawa a baya.
Zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu, da Dokta Ngozi Okonjo-Iweala, babbar darakta a Cibiyar kasuwanci ta duniya, sun shiga jerin mutane 100 da suka fi tasiri a duniya na shekarar 2023 da Mujallar Time ta fitar.
Ana ci gaba da maida martani game da tuhumar Donald Trump a Amurka inda kawuna suka rabu, wannan dai shi ne karon farko da ake tuhumar wani tsohon shugaba a Amurka.
Masu taimaka wa alkali yanke hukunci na Manhattan (birnin New York) sun tuhumi Donald Trump kan kudin toshiyar baki da aka biya Stormy Daniel.
Shugaba Joe Biden ya bude taron koli na Dimokuradiyya karo na biyu a jiya Laraba, inda ya yi alkawarin cewa Amurka za ta kashe dala miliyan $690M a shekara mai zuwa domin bunkasa shirye-shiryen dimokradiyya a fadin duniya.
Mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris, za ta gana da 'yan kasuwa mata na kasar Ghana a yau Laraba, don tattaunawa kan karfafa tattalin arziki da jagoranci,
A yau ne wata kotu a Amurka ta yanke wa wani dan Najeriya mai suna Solomon Ekunke Okpe, dan shekaru 31, hukuncin daurin shekaru hudu da wata daya a gidan yari, bisa samunsa da hannu a wata kungiyar masu aikata laifuka ta yanar gizo.
Fiye da bakin haure talatin da tara ne suka mutu sanadiyyar gobara a wata cibiyar ajiye bakin haure da ke arewacin Mexico a kusa da kan iyakar Amurka, in ji wani jami'i ranar Talata.
Yau Litinin wata mace ‘yar bindiga ta kashe yara 3 da manyan mutane 4, a makarantar Christian grade a jihar Tennessee da ke kudancin Amurka, kamar yadda hukumomi suka bayyana.
Sakataren harakokin wajen Amurka Antony Blinken da ke ziyarar wuni biyu a jamhuriyar Nijar ya sanar da karin kudaden tallafi ga kasashen yammaci da tsakiyar Afrika wadanda za'a yi amfani da su don inganta rayuwar al’umomin wadannan kasashe.
Domin Kari