Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Tur Da Kisan Jami’an Ofishin Jakadancinta, Ta Kuma Kuduri Aniyar Ganin An Ceto Wadanda Suka Bace


Sakataren gwamnatin Amurka Anthony Blinken
Sakataren gwamnatin Amurka Anthony Blinken

Tawagar jami'an da aka kai wa hari ranar Talata a garin Ogbaru na jihar Anambra ta kunshi ‘yan Najeriya guda tara, ciki har da ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka a Najeriya biyar da kuma jami’an ‘yan sandan Najeriya hudu.

Jami'an sun yi tafiyar ne gabanin wata ziyara da jami’an ofishin jakadancin Amurka suka shirya kai wa don wani shiri na taimaka wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, wanda Amurka ta dauki nauyinsa a jihar Anambra.

A cikin wata sanarwa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony J. Blinken ya fitar, Amurka ta ce har yanzu ba a san dalilin kai harin ba, amma a halin yanzu babu wata alama da ke nuna cewa an auna ofishin jakadancin ne.

Maharan sun kashe akalla mutane hudu daga cikin tawagar, kuma jami’an ofishin jakadancin Amurka na aiki tare da takwarorinsu na Najeriya domin gano wuri da halin da sauran jami’an da ba a gani ba suke.

"Muna Allah wadai da wannan harin. Za mu yi aiki kusa-da-kusa da jami'an tsaron Najeriya don hukunta wadanda suka kai shi, a cewar sanarwar.

"Amurka ba ta da abinda ta fi ba fifiko kamar tsaron ma'aikatanmu. Muna mika ta'aziyyarmu ga iyalan wadanda aka kashe a harin, kuma mun yi alkawarin yin duk mai yiwuwa don maido da sauran wadanda suka bace.

Sanarwar ta kara da cewa, muna matukar mutunta dangantakarmu da ma'aikatanmu na Najeriya da kuma kawancenmu da kasar.

Amurka ta jaddada aniyarta ga al'ummar Najeriya ta taimaka wa wajen kawar da tashe-tashen hankula da rashin tsaro a kasar, a cewar Blinken.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG